- IPOB ta ce shugabancin Buhari na kama karya zai ruguza Najeriya.
- Kungiyar mai goyon bayan kafa kasar Biafara ta yi gargadi cewa mummunan rikici na dab da faruwa a Najeriya

kungiyar 'yan asalin yankin Biafara (IPOB) ta yi gargadi game da Buhari
Kungiyar
ta ce Najeriya ka iya fuskantar tashin hankali sanadiyyar salon mulkin
kama karya na shugaba Muhammadu Buhari, su na masu bayar da misali da
kin sakin shugabansu Nnamdi Kanu daga tsarewar da a ke masa.
Vanguard
ta rawaito cewa hakan na dauke ne a wata sanarwa da Sakataren yada
labaran kungiyar, Comrade Emma Powerful ya sanya wa hannu, a ranar
Talata 3 ga watan Janairu.
Powerful ya kuma ce
sakin fefayen bidiyo na tonon asirin abubuwan da a ke ba dai-dai ba a
kasar nan zai ci gaba da bankado gaskiyar da a ke boyewa wadanda ka iya
rusa Najeriya kamar yadda Nnamdi Kanu ya yi barazana.
No comments:
Post a Comment