-
Wadanda aka sake sune Salem Ahmad Hadi Bin Kanad, Muhammed Rajab Sadiq
Abu Ghanim, Abdallah Yahya Yusif Al-Shibli, da Muhammad Ali Abdallah
Muhammad Bwazir
- Shugaba mai jiran gado,Donald Trump yayi Allah wadai da wannan abu

Obama ya saki wasu fursunonin Guantanamo 4
A jiya Alhamis, 5 ga watan Junairu,
shugaban kasan Amurka, gwamnatin Barack Obama ta sanar da cewa zata saki
ursunonin Gwantanamo 4 wanda Donald Trump yayi Allah wadai da wannan.
Fursunonin da aka saki yan kasan Yemen ne kuma yace kai su kasar Saudiyya ,akwai sauran fursunoni sama da 50 a Guantanamo.
Game
da cewar ma’aikatar tsaron Amurka. Wadanda aka saki sune Salem Ahmad
Hadi Bin Kanad, Muhammed Rajab Sadiq Abu Ghanim, Abdallah Yahya Yusif
Al-Shibli, da Muhammad Ali Abdallah Muhammad Bwazir.
KU KARANTA: Anyima fursunoni 10,000 afuwa
Jawabin
ma’aikatar tace: Kamar yadda shugaban kasa ya bada umurni a Junairun
2009, akan duba yadda za’a sake duba zancen fursunonin. Bayan an duba
abubuwan an amince a saki wasu fursunonin.
Amma,
shugaban kasa mai jiran gado, Donald Trump, yace kada a sake fitar da
wani fursuna daga gidan yarin Guantanamo Bay dake kasar Kuba.
“Kada a sake fito da mutane daga Gitmo. Wadannan mutane ne asu hadari kuma kada a bari ku koma cikin jama’a."
A bangare guda, hukumar sojin Amurka ta amincewa soji musulmai su bar gemu ,kuma mata sun sanya hijabinsu.
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
No comments:
Post a Comment